Genesis 46:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنَّنْ سُونٜىٰ یَیَ مَذَنْ دَ بِلْهَ تَحَيْڢَا وَ يَعْڧُوبَ؞ بِلْهَ ثٜىٰ بَيْوَرْ دَ لَبَنْ يَبَا رَحِيلَةُ أَ لُواْكَثِنْ عَوْرٜىٰنْتَ؞ یَیَنْتَ دُكَ، مُتُمْ بَݣَويْ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa 'yarsa Rahila.