Genesis 46:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Yaƙub ya bar Beyersheba, ’ya’yan Isra’ila maza, suka ɗauki mahaifinsu Yaƙub da ’ya’yansu da matansu a cikin wagonun da Fir’auna ya aika don a kawo shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَعْڧُوبَ يَتَاشِ دَغَ بٜىٰيٜىٰرْشٜىٰبَ، یَیَنْسَ مَظَا كُوَ سُكَ طَوْكِ بَابَنْسُ يَعْڧُوبَ دَ يَارَنْسُ ڧَنَانَا دَ مَاتَنْسُ عَثِكِنْ كٜىٰكُنَنْ شَانُنْ دَ ڢِرْعَوْنَ يَعَيْكَ أَطَوْكُواْ شِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, 'ya'yan Isra'ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da 'yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir'auna ya aika a ɗauko su.