Genesis 47:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَعْڧُوبَ كُوَ يَا ذَوْنَ شٜىٰكَرَا غُواْمَشَا بَݣَويْ عَڧَسَرْ مَصَرْ؞ ݣُونَكِنْ يَعْڧُوبَ كُوَ شٜىٰكَرَا ثٜىٰ طَرِے دَ أَرْبَعِنْ دَ بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Masar shekara goma sha bakwai, don haka kwanakin Yakubu, wato shekarun ransa, shekara ce ɗari da arba'in da bakwai.