Genesis 47:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?” Suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Bayinka makiyaya ne, kamar yadda kakanninmu suke.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِرْعَوْنَ يَتَمْبَيِ یَنْعُوَنْ يُوسُڢَ يَثٜىٰ «مٜىٰنٜىٰنٜىٰ عَيْكِنْكُ؟» سُكَ أَمْسَوَ ڢِرْعَوْنَ سُكَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، مُو مَكِيَايَنْ دَبُّواْبِے نٜىٰ كَمَرْ كَاكَنِّنْمُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Fir'auna ya ce wa 'yan'uwan nan nasa, “Mece ce sana'arku?” Suka amsa wa Fir'auna, suka ce, “Ranka ya daɗe, mu makiyaya ne, kamar yadda iyayenmu suke.”