Genesis 48:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu fa idanun Isra’ila sun fara rasa ƙarfi saboda tsufa, har ba ya iya gani sosai. Saboda haka Yusuf ya kawo ’ya’yansa maza kusa da shi, sai mahaifinsa ya sumbace su ya rungume su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِدَانُنْ إِسْرَٰٓءِيلَ يَنْذُ سُنْيِ دُهُ سَبُواْدَ يَوَنْ ڟُوڢَرْسَ حَرْ بَا يَ عِيَ غَنِ سُواْسَيْ؞ سَيْ يُوسُڢَ يَكَٰوُاْ یَیَنْسَ كُسَدَشِ؞ سَيْ إِسْرَٰٓءِيلَ يَيِ مُسُ سُمْبَ يَضُنْغُمٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu fa, idanun Isra'ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su.