Genesis 48:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا بَابَنْسَ يَڧِ ثٜىٰوَ «أَيْ، نَاسَنِ طَانَ، نَاسَنِ؞ شِمَا ذَيْ ذَمَ ذُرِيَ، ذَيْ ذَمَ مَيْغِرْمَ؞ دُكْدَهَكَ ڧَنٜىٰنْسَ ذَيْڢِيشِ غِرْمَ، ذُرِيَرْسَ كُمَ ذَاسُ ذَمَ تَارُوانْ أَلْعُمَّيْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma mahaifinsa ya ƙi, ya ce, “Na sani, ɗana, na sani, shi ma zai zama al'umma, zai ƙasaita, duk da haka ƙanensa zai fi shi ƙasaita, zuriyarsa kuwa za ta zama taron al'ummai.”