Genesis 49:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Albarkun mahaifi suna da girma fiye da albarkun daɗaɗɗun duwatsu fiye da yalwar madawwaman tuddai. Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin ɗan sarki a cikin ’yan’uwansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْبَرْكُنْ بَابَنْكَ سُڢِ أَلْبَرْكُنْ دُوَڟُو مَاسُ دَوَّمَ دَ أَلْحٜىٰرَنْ تُدَّيْ نَتُنْتُنِ؞ بَرِ سُكَسَنْثٜىٰ عَبِسَ كَنْكَ، يُوسُڢَ، أَغُواْشِنْ وَنْدَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ، وَنْدَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَغَ یَنْعُوَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Albarkun hatsi da na gari Albarkun daɗaɗɗun duwatsu, Abubuwan jin daɗi na madawwaman tuddai, Allah ya sa su zauna a kan Yusufu, Da a goshin wanda aka raba shi da 'yan'uwansa.