Genesis 50:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka, kada ku ji tsoro. Zan tanada muku da kuma ’ya’yanku.” Ya sāke tabbatar musu, ya kuma yi musu magana ta alheri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ كَدَ كُجِڟُواْرُواْ؞ ذَنْتَنَدَ مُكُ دَ يَارَنْكُ ڧَنَانَا؞» تَهَكَ يَتَعَظَنْتَرْ دَسُو يَيِمُسُ مَغَنَ مَيْ ݣُونْتَرْدَ ذُوثِيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka kada ku ji tsoro, zan tanada muku, ku da ƙanananku.” Ta haka ya ta'azantar da su, ya yi musu magana ta kwantar da zuciya.