Genesis 6:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، نِے ذَنْعَيْكَ دَ بَبَّرْ أَمْبَلِيَرْ ضُوَ عَدُونِيَا، وَدَّ ذَاتَ هَلَّكَ كُواْوَثٜىٰ حَلِتَّ مَيْ رَيْ عَڧَرْڧَشِنْ سَمَ؞ كُواْوَنٜىٰ أَبُ عَدُونِيَا ذَيْ مُتُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu.