Genesis 6:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ «غَبَاطَيَ ذَنْكَوَرْدَ دُكَنْ یَنْ أَدَمْ وَطَنْدَ نَحَلِتَّ دَغَ ڢُسْكَرْ دُونِيَا؞ دَغَ یَنْ أَدَمْ ذُوَا دَبُّواْبِے دَغَ حَلِتُّو مَاسُ رَرَّڢٜىٰ عَڧَسَا ذُوَا ڟُنْڟَيٜىٰنْ سَرَرِنْ سَمَ، غَمَا إِنَ بَڧِنْ ثِكِ دَ نَحَلِثّٜىٰسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.”