Genesis 7:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tare da su kuwa, akwai kowane naman jeji bisa ga irinsa, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinta, da kowane tsuntsun gida da na jeji bisa ga irinsa, da dukan abu mai fiffike.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَرٜىٰدَسُو كُوَ أَݣَويْ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ دَبَّرْ دَاجِ بِسَغَ إِرِنْسَ دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ دَبَّرْ غِدَا بِسَغَ إِرِنْسَ دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ أَبُ مَيْ رَرَّڢٜىٰ عَڧَسَا بِسَغَ إِرِنْسَ دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ ڟُنْڟُ بِسَغَ إِرِنْسَ دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ دَبَّ مَيْ ڢِكَڢِكَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi.