Habakkuk 1:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan tā da Babiloniyawa, waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri, waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، إِنَ تَادَ كَلْدِيَاوَا، أَلْعُمَّرْ نَنْ مَيْ ذَاڢِنْ رَيْ مَيْ ڢِتِنَ كُمَ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ تَڢِيَ كُواْعِنَ أَ ڢَاطِنْ دُونِيَا سُڨُوثٜىٰ وُرَارٜىٰنْ ذَمَنْ دَ بَنَاسُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shi, ina tā da Kaldiyawa, Al'umman nan mai zafi, mai fitina, Waɗanda suke tafiya ko'ina a duniya, Sun ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.