Habakkuk 3:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba, ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi, ko da yake zaitun bai ba da amfani ba, gonaki kuma ba su ba da abinci ba, ko da yake babu tumaki a garke, ba kuma shanu a turaku,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْدَيَكٜىٰ إِتَاثٜىٰنْ ٻَوْرٜىٰ بَيْيِ ڢُلَوَبَ، كُمَبَا یَیَ عَكَنْ إِتَاثٜىٰنْ إِنَبِے، كُواْدَيَكٜىٰ إِتَاثٜىٰنْ ظَيْتُنْ بَيْ بَادَ أَمْڢَانِبَ، كُمَ غُواْنَكِ بَسُ بَادَ أَمْڢَانِبَ، كُواْدَيَكٜىٰ بَابُ تُمَكِ أَغَرْكٜىٰنْسُ، كُمَ بَابُ شَانُو أَوُرِنْ ذَمَنْسُ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba, Ba kuma 'ya'ya a kurangar inabi, Zaitun kuma bai ba da amfani ba, Gonaki ba su ba da abinci ba, An kuma raba garken tumaki daga cikin garke, Ba kuma shanu a turaku,