Haggai 1:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, wanda yake babban firist, da kuma dukan raguwar jama’ar suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu da kuma saƙon annabi Haggai, domin Ubangiji Allahnsu ne ya aiko shi. Mutane kuwa suka ji tsoron Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ظٜىٰرُبَّبٜىٰلْ طَنْ شٜىٰيَلْتِيٜىٰلْ دَ يُواْشُوَ طَنْ يٜىٰهُواْظَدَكْ بَبَّنْ ڢِرِسْتِ، تَرٜىٰدَ دُكَنْ ضَغُواْوَرْ جَمَعَرْ سُكَيِ بِيَيَّ دَ مُرْيَرْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسُ، سُكَ كُمَيِ بِيَيَّ دَ مَغَنَرْسَ تَبَاكِنْ أَنَّبِے هَغَّيْ وَنْدَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسُ يَعَيْكَ؞ سَيْ ڟُواْرُوانْ يَهْوٜىٰهْ كُوَ يَكَامَ جَمَعَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji.