Haggai 1:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ga shi, kukan sa rai za ku sami da yawa, amma sai ku ga kun sami kaɗan. Ɗan kaɗan ɗin ma da kukan kawo gida, nakan hura shi yă tafi. Me ya sa yake faruwa haka?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Saboda gidana da yake zaman kango, yayinda kowannenku yana faman gina gidansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹غَاشِ، كُكَنْ سَا رَيْ ذَاكُ سَامِ دَيَوَ، عَمَّا سَيْ كُغَ كُنْ سَامِ كَطَنْ؞ طَنْ كَطَنْ طِنْ مَا دَ كُكَنْ كَٰوُاْ غِدَا، نَكَنْ هُورَ شِ يَتَڢِے؞ مٜىٰيَسَا يَكٜىٰ ڢَرُوَ حَكَ؟ سَبُواْدَ غِدَانَ دَ عَكَبَرِ كُڢَيْ نٜىٰ! عَمَّا كُواْوَنّٜىٰنْكُ يَنَ ڢَامَ دَ غِنِنْ غِدَنْسَ،› إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Kun sa zuciya za ku sami da yawa, sai kuka sami kaɗan. Sa'ad da kuma kuka kawo shi gida, sai na hurar da shi. Me ya sa haka? Saboda Haikalina da yake zaman kufai, amma ko wannenku yana fama da ginin gidansa.