Hebrews 11:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْ بَاتَرٜىٰدَ بَنْ‌غَسْكِيَابَ، بَايَ يِوُوَ أَ ڢَرَنْتَاوَا اللَّهْ رَيْ، غَمَا دُكْ مَيْ مَڟُواْوَ كُسَدَ اللَّهْ دُواْلٜىٰنٜىٰ يَبَادَ غَسْكِيَ ثٜىٰوَ أَݣَويْ اللَّهْ كُمَ يَنَ بَادَ لَادَ غَ دُكْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ نٜىٰمَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
In ba a game da bangaskiya ba kuwa, ba shi yiwuwa a faranta masa rai. Domin duk wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata cewa, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa.