Hebrews 6:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ ڧَسَا تَنَ ڢِتَرْدَ ڧَيَ دَ مُوغُوَرْ ثِيَوَ، بَاتَدَ أَمْڢَانِ كٜىٰنَنْ؞ وَنَّنْ ڧَسَا كُوَ اللَّهْ يَكُسَ يَلَعَنْتَتَ؞ عَڧَرْشٜىٰ كُمَ ڧُواْنٜىٰتَ ذَاعَيِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma tsire-tsirenta ƙaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, ƙarshenta dai ƙonewa ne.