Hebrews 8:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا يَنْذُ أَنْبَا عِيسَىٰ عَيْكِنْ ڢِرِسْتِ وَنْدَ يَكٜىٰ مَڢِے ݣَوْ، كَمَرْ يَدَّ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ نَنْ تَكٜىٰ مَڢِے ݣَوْ، وَدَّ عِيسَىٰ شِينٜىٰ مَيْ ڟَيَاوَا ڟَكَانِنْ اللَّهْ دَ مُتَنٜىٰ؞ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ نَنْ كُوَ مَڢِے ݣَوْ ثٜىٰ غَمَا أَنْكَڢَتَ عَكَنْ أَلْكَوَرَنْ دَ سُنْڢِے ݣَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ga ainihi, Almasihu ya sami hidima wadda take mafificiya, kamar yadda alkawarin nan,wanda shi ne matsakancinsa, yake da fifiko nesa, tun da yake an kafa shi ne a kan mafifitan alkawarai.