Hebrews 9:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْدَ مُوسَٰى يَسَنَرْ وَدُكَنْ جَمَعَ كُواْوَنٜىٰ عُمَرْنِنْ دَيَكٜىٰ ثِكِنْ كُواْيَرْوَرْ، سَيْ يَطَوْكِ جِنِنْ یَیَنْ شَانُو دَ نَأَوَكِ، يَهَطَ دَ ضُوَ؞ سَعَنً يَطَوْكِ سُواْسُوانْ إِظُوابْ تَرٜىٰدَ جَنْ غَاشِنْ تُمَكِ يَيَيَّڢَا جِنِنْ عَكَنْ لِتَّڢِنْ كُواْيَرْوَا دَ كُمَ عَكَنْ دُكَنْ جَمَعَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don bayan Musa ya sanar da kowane umarnin Shari'a ga dukan jama'a, sai ya ɗebi jinin 'yan maruƙa da na awaki, tare da ruwa, da jan ulu, da kuma ganyen izob, ya yayyafa wa Littafin kansa, da kuma duk jama'a,