Hebrews 9:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنْ كَڢَ تٜىٰنْتِ وَنْدَ يَكٜىٰدَ سَاشٜىٰ نَڢَرْكُواْ، عِنْدَ عَكَسَا سَنْدَا مَيْ رِڧٜىٰ ڢِتِلُ دَ تٜىٰبُرْ دَ غُرَاسَرْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ؞ وَنَّنْ سَاشٜىٰ كُوَ شِينٜىٰ عَكٜىٰثٜىٰ دَشِ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wato, an kafa alfarwa wadda sashinta na farko yake da fitila, da tebur, da kuma keɓaɓɓiyar gurasa. Ana kiran wannan sashi Wuri Mai Tsarki.