Hebrews 9:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ وَنَّنْ سَاشٜىٰ كُوَ أَݣَويْ بَغَدٜىٰنْ دَ عَكَنْ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ مَيْ ڧَنْشِ عَكَيْ دَ كُمَ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ؞ وَطَنَّنْ أَبُ بِيُ كُوَ أَنْشَاڢٜىٰسُ دَ ظِينَارِيَ؞ عَثِكِنْ عَݣُوتِنَّنْ نَيَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ كُوَ أَݣَويْ ݣُونُوانْ ظِينَارِيَ دَ مَنَّ عَثِكِ دَ سَنْدَنْ هَٰرُونَ وَنْدَ يَڢِتَرْدَ غَنْيٜىٰ دَ أَلُّنَنْ دُوڟٜىٰ بِيُ نَيَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A cikinsa kuwa da faranti na zinariya domin ƙona turare, da kuma akwatin alkawari da aka yi masa laffa da zinariya ta kowane gefe. A cikinsa kuwa akwai tasar zinariya da manna a ciki, da sandar Haruna wadda ta yi toho, da kuma allunan dutse na alkawarin nan.