Hosea 1:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢَرْكُوانْ سَڧُوانْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا وَ يُوشَعُ شِينٜىٰ «كَتَڢِے كَعَوْرِ كَارُوَ، كَحَيْڢِ یَیَنْ كَارُوَنْثِ؞ غَمَا تَهَكَ مُتَنٜىٰنَ سُنْشِغَ كَارُوَنْثِ سُواْسَيْ تَوُرِنْ ڧِينَ،» إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Ubangiji ya fara yin magana da Yusha'u ya ce masa, “Tafi ka auro karuwa, ka haifi 'ya'yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.”