Hosea 12:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi; shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَسَا اللَّهْ يَيِ ڢُشِے سُواْسَيْ، عُبَنْ‌غِجِنْسُ ذَيْسَاكَ مُسُ عَكَنْ لَيْڢُواْڢِنْسُ، دَ كُنْيَرْ دَسُكَ جَٰوُاْ مَسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen Ifraimu sun yi muguwar tsokana mai ta da fushi, Domin haka Ubangiji zai ɗora musu hakkin jini a kansu, Zai saka musu cin mutuncin da suka yi.