Hosea 14:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutane za su sāke zauna a inuwarsa. Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi. Zai yi fure kamar kuringa, zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنْدَ سُكَذُواْ سُذَوْنَ عَڧَرْڧَشِنْ إِنُوَرْسُ، ذَاسُيِ نُواْمَنْ حَڟِ دَيَوَ، سُيِ یَیَ كَمَرْ إِتَاثٜىٰنْ إِنَبِے؞ ڧَنْشِنْسُ ذَيْسَامِ سُنَ كَمَرْ ضُوً إِنَبِے نَ لٜىٰبَنُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗanda za su komo, za su zauna a inuwarta, Za su yi noman hatsi da yawa. Za su yi fure kamar kurangar inabi. Ƙanshinsu zai zama kamar ruwan inabi na Lebanon.