Hosea 2:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan tsayar da dukan bukukkuwarta, bukukkuwarta na shekara-shekara, da kuma kiyaye bikin Sababbin Wata nata, kwanakin Asabbacinta, dukan ƙayyadaddun bukukkuwarta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْكَٰوُاْ ڧَرْشٜىٰنْ ڢَضٍ ثِكِنْتَ، دَ بُكُكُوَنْتَ نَشٜىٰكَرَا شٜىٰكَرَا، دَ نَسَابُوانْ وَتَ دَ نَهُتُ تَمَكُواْ، دَ دُكْ دَيْ بُكُكُوَنْتَ نَمُسَمَّنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan sa ta daina farin cikinta, Da idodinta, da kiyaye lokatan amaryar wata, Da hutawar ranar Asabar, Da ƙayyadaddun idodinta.