Hosea 2:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna, da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa. Zan karɓe ulu nawa da lilina, da take niyya ta rufe tsiraicinta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، ذَنْ كَرْٻِ حَڟِنَ لُواْكَثِنْدَ يَ إِسَ غِرْبِے، دَ ضُوً إِنَبِنَ دَيْدَيْ لُواْكَثِنْسَ؞ عِ، ذَنْݣُوشِ عُلُونَ دَ لِيلِنَ دَ نَبَاتَ دُواْمِنْ تَطِنْكَ رِغَرْ رُڢٜىٰ ڟِرَيْثِنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa, Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilin Waɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.