Hosea 3:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَڧُواْ نَبِيُ وَنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَعَيْكَ مِنِ شِينٜىٰ «كَتَڢِے، كَثِيغَبَدَ نُونَ ڧَوْنَرْكَ غَ مَاتَرْكَ نَنْ وَدَّ تَكٜىٰبِنْ مَظَا تَنَ ظِنَ دَسُو؞ كَڧَوْنَثٜىٰتَ كَمَرْ يَدَّ نِے يَهْوٜىٰهْ نَكٜىٰ ڧَوْنَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كُواْدَيَكٜىٰ تَجُويَ غَ بِنْ وَطَنْسُ أَلُّواْلِ تَنَ ݣُوطَيِنْ بُوسَسُّنْ یَیَنْ إِنَبِنْدَ عَكَ مِيڧَا وَ غُمَكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka sāke tafiya, ka ƙaunaci karuwa wadda take tare da kwartonta. Ka ƙaunace ta kamar yadda ni Ubangiji nake ƙaunar mutanen Isra'ila, ko da yake suna bin gumaka, suna ƙaunar wainar zabibi da aka miƙa wa gumaka.”