Hosea 4:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai, a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri, inda inuwa take da daɗi. Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنَ مِيڧَ هَدَايُ غَ غُمَكَ عَكَنْ مَنْيَنْ تُدَّيْ؞ سُنَ هَوَنْ تُدَّيْ سُڧُواْنَ تُرَارٜىٰ عَڧَرْڧَشِنْ إِنُوَ مَيْݣَوْ تَ إِتَاثٜىٰنْ ڟَاڢِ دَ تَدَرْغَظَ، دَ تَ إِتَاثٜىٰ مَرَرْ بُوشٜىٰوَ؞ «دُواْمِنْ حَكَ یَیَنْكُ مَتَ سُنْ شِغَ كَارُوَنْثِ، مَتَنْ یَیَنْكُ كُمَ سُنْ شِغَ ظِنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suna miƙa sadaka a bisa ƙwanƙolin duwatsu. Suna yin hadaya a bisa tuddai, Da kuma a gindin itacen oak, da aduruku, da katambiri, Domin suna da inuwa mai kyau. Don haka 'ya'yanku mata suke karuwanci, Surukanku mata suke yin zina.