Hosea 5:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Sa’ad da Efraim ya ga ciwonsa, Yahuda kuwa miyakunta, sai Efraim ya juya ga Assuriya, ya aika wurin babban sarki don neman taimako. Amma bai iya warkar da kai ba, bai iya warkar da miyakunka ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُلْكٍ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَغَ ثِيوُانْسُ، مُلْكٍ يَهُودَ كُمَ سُكَغَ رَوْنِنْسُ، سَيْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُنْ عَيْكَ نٜىٰمَنْ تَيْمَكُواْ أَعَسُّرِيَ وُرِنْ بَبَّنْ سَرْكِے؞ عَمَّا بَبَّنْ سَرْكِنْ بَيْ عِيَ تَيْمَكُواْ كُواْ وَرْكَرْدَ ثِيوُانْسُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sa'ad da Ifraimu ta ga ciwonta, Yahuza kuma ta ga rauninta, Sai Ifraimu ta aika zuwa Assuriya, Wurin babban sarki. Amman ba zai iya warkar da ciwonki, ko rauninki ba.