Hosea 5:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da suka tafi tare da garkunan shanu, tumaki da awakinsu don su nemi Ubangiji, ba za su same shi ba; ya janye kansa daga gare su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ غَرْكُنَنْسُ نَتُمَكِ دَ نَشَانُو ذَاسُ تَڢِے نٜىٰمَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ عَمَّا بَذَاسُ سَامٜىٰنِبَ، غَمَا ذَنْ جَنْيٜىٰ كَيْنَ دَغَ غَرٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da garkunan tumaki da na awaki, da na shanunsu Za su tafi neman Ubangiji, Amma ba za su same shi ba, Gama ya rabu da su.