Hosea 7:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zukatansu suna kamar matoya; sukan kusace shi da wayo. Muguwar aniyarsu takan yi ta ci dukan dare; da safe sai ta ƙuna kamar harshen wuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذُوثِيَارْسُ سُنَ ذَاڢِ كَمَرْ وُتَرْ تُواْيَ غُرَاسَ؞ ڢُشِنْسُ يَكَنْيِ تَثِ دَدَرٜىٰ، دَ سَڢٜىٰ كُمَ سَيْ يَبُوطٜىٰ كَمَرْ هَرْشٜىٰنْ وُتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu. Fushinsu na ci dare farai, Da safe fushinsu yana ci bal-bal kamar harshen wuta.