Hosea 8:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya! Fushina yana ƙuna a kansu. Sai yaushe za su rabu da gumaka?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كٜىٰ سَمَرِيَ، نَڧِ غُنْكِنَّنْ، مَيْ صِڢَّرْ طَنْ سَانِيَ دَ كِكٜىٰ دَشِ؞ ڢُشِنَ يَتَاشِ عَكَنْكِ؞ سَيْ يَوْشٜىٰ ذَاكِ دَيْنَ يِنْ أَيُّكَنْ ڧَظَنْتَا؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya mutanen Samariya, ina ƙin maraƙinku na siffa. Ina jin haushinsu ƙwarai! Sai yaushe za su rabu da gumaka?