Isaiah 1:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dubi yadda amintacciyar birni ta zama karuwa! Dā ta cika da yin gaskiya; dā masu adalci a can suke zama, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai!
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَيَّ! يَيَ بِرْنِ مَيْ أَمِنْثِ أَدَا يَذَمَ كَمَرْ مَثٜىٰ مَيْ ثِنْ أَمَانَ؟ أَ دَا ثَنْ يَنَ ثِكٜىٰ دَ غَسْكِيَ، دَا مَا ثِكٜىٰ دَ أَدَلْثِے يَكٜىٰ، عَمَّا يَنْذُ ثِكٜىٰ يَكٜىٰدَ مَاسُ كِسَنْ كَيْ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai.