Isaiah 10:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai; kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai, haka na tattara dukan ƙasashe; ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki, ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَمَرْ يَدَّ مُتُمْ يَسَا حَنُّ دُواْمِنْ يَݣُوشٜىٰ ڨُويْ دَغَ غِدَنْ ڟُنْڟُنْدَ بَعَڟَرٜىٰبَ، حَكَ نَسَا هَنُّونَ عَثِكِنْ ڧَسَاشٜىٰ نَݣُوشٜىٰ دُوكِيَرْسُ، حَكَ نَتَتَّارَ دُكَنْ ڧَسَاشٜىٰنْ دُونِيَا؞ بَابُ مَيْ كَطَ ڢِكَڢِكَيْ، كُواْ مَيْ بُوطٜىٰ بَاكِ دُواْمِنْ كُوكَنْ ڟَرٜىٰ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Al'umman duniya kamar sheƙar tsuntsaye suke. Na tattara dukiyarsu, a sawwaƙe kamar yadda ake tattara ƙwai, ba tsuntsun da ya buɗe baki don ya yi mini kuka!”