Isaiah 10:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta, Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta; a rana guda zai ƙone yă kuma cinye ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
اللَّهْ حَصْكٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذَيْ ذَمَ وُتَا، مَيْ ڟَرْكِے نَ إِسْرَٰٓءِيلَ هَرْشٜىٰنْ وُتَا، أَ رَانَ طَيَ، ذَيْ ڧُواْنٜىٰ كُواْوَنٜىٰ أَبُ حَرْ دَ ڧَيُواْيِ دَ وُتَا وُتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah da yake hasken Isra'ila, zai zama wuta. Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, zai zama harshen wuta, wanda zai ƙone kowane abu rana ɗaya, har da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.