Isaiah 11:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai tā da tuta saboda al’ummai yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila; zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse kusurwoyi huɗu na duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ ذَيْ تَادَ تُوتَ عَلَمَثٜىٰ تَتَتَّارَ أَلْعُمَّيْ، ذَيْ تَارَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَطَنْدَ عَكَ كُواْرَ، مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ وَطَنْدَ عَكَ وَاڟَرْ كُمَ يَتَتَّارَ دَغَ دُكَنْ ݣُونَ حُطُ نَدُونِيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji zai ɗaga tuta, alama ce ta nuna wa sauran al'umma, ya sāke tattara jama'ar Isra'ila da ta Yahuza waɗanda aka warwatsa, ya sāke komo da su daga kusurwoyi huɗu na duniya.