Isaiah 11:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji zai busar da bakin tekun Masar; da iska mai zafi zai share hannunsa a bisa Kogin Yuferites Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai saboda mutane su iya hayewa da ƙafa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ ذَيْسَا تٜىٰكُنْ ثِيَوَرْ إِوَ نَ مَصَرْ يَبُوشٜىٰ، يَمِيڧَ حَنُّنْسَ يَسَا إِسْكَ مَيْ ذَاڢِ تَهُورَ عَكَنْ كُواْغِنْ يُڢِرٜىٰتِسْ؞ ذَيْسَا كُواْغِنْ يَرَبُ حَرْ كَشِ بَݣَويْ يَدَّ مُتَنٜىٰ ذَاسُ عِيَ ڧٜىٰتَرٜىٰوَ دَ ڧَڢَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji zai kawo iska mai zafi wadda za ta busar da Kogin Nilu, da na Yufiretis. Zai bar ƙananan rafuffuka bakwai ne kaɗai, don kowa da kowa ya taka ya haye.