Isaiah 11:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا دَ أَدَلْثِے ذَيْ يِوَتَلَكَاوَا شَرِيعَ، يَكُمَ ڟَرٜىٰ حَكِّنْ مَرَسَ ڧَرْڢِے؞ دَ مَغَنَرْ بَاكِنْسَ ذَيْ حُكُنْتَ ڧَسَا، دَ نُمْڢَشِنْ بَاكِنْسَ ذَيْ بُغِ مُوغَيٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai yi wa matalauta shari'a daidai. Zai kuma kāre hakkin masu tawali'u. Bisa ga umarninsa za a hukunta ƙasar, Mugaye za su mutu.