Isaiah 13:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili, ka tā da murya gare su; ka ɗaga hannu ka ba su alama don su shiga ƙofofi masu alfarma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَنْ تُدُ مَرَرْ كُواْمٜىٰ عَتَادَ تُوتَرْ يَاڧِ! عَتَادَ مُرْيَ غَ مَاسُ يَاڧِ، أَطَغَ حَنُّ عَبَاسُ عَلَمَ سُشِغَ يَاڧِ عَڧُواْڢُواْڢِنْ بِرْنِنْ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kan tudun da yake faƙo ka kafa tutar yaƙi, ka ta da murya ka ba mayaƙa umarni, ka ɗaga hannu, ka ba su alamar kama yaƙi a ƙofofin birni mai alfarma.