Isaiah 13:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu, sai ka ce na babban taron jama’a! Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki, sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa! Ubangiji Maɗaukaki yana shirya mayaƙa don yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
جِ هَيَانِيَرْ دَ عَكٜىٰيِ عَتُدَّيْ كَمَرْ تَبَبَّنْ تَارُواْ؞ جِ إِيهُ نَتَارُوانْ مَاسُ مُلْكِ، إِيهٌ تَارُوَرْ أَلْعُمَّيْ؞ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا نٜىٰ يَكٜىٰ تَتَّارَ ضُنْدُنَارْ سُواْجُواْجِنْ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ji hayaniyar da ake yi a duwatsu da amon babban taron jama'a. Amon al'ummai da mulkoki suna tattaruwa. Ubangiji Mai Runduna yana shirya mayaƙansa domin yaƙi.