Isaiah 14:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai; zai sāke zaɓi Isra’ila yă kuma zaunar da su a ƙasarsu. Baƙi ma za su zo su zauna tare da su su haɗa kai da gidan Yaƙub.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا يَهْوٜىٰهْ ذَيْجِے تَوْسَيِنْ ذُرِيَرْ يَعْڧُوبَ؞ يَهْوٜىٰهْ ذَيْسَاكٜىٰ ذَاٻٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ تَذَمَ جَمَعَرْسَ تَمُسَمَّنْ، ذَيْ كُمَ سَاسُ سُذَوْنَ عَڧَسَرْسُ؞ بَاڧِ ذَاسُ حَطَكَيْ دَسُو، سُمَنّٜىٰوَ غِدَنْ يَعْڧُوبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su.