Isaiah 14:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Zan yi gāba da su,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta, ’ya’yanta da zuriyarta,” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ، «ذَنْ ڢَاطَوَ بَابِيلَ دَ يَاڧِ، إِنْ كَوَرْدَ سُونَنْتَ دَ ضَغُواْوَرْتَ، یَیَنْتَ دَ جِيكُواْكِنْتَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan fāɗa wa Babila da yaƙi, in lalata ta, ba abin da zan bari, ko yara, ba wanda zai ragu. Ni, Ubangiji, na faɗi wannan.