Isaiah 15:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Heshbon da Eleyale sun yi kuka da ƙarfi, aka ji muryoyinsu ko’ina har zuwa Yahaz. Saboda haka mayaƙan Mowab suka yi kuka da ƙarfi, har zuciyarsu ta karai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ هٜىٰشْبُوانْ دَ نَ عٜىٰلٜىٰيَلٜىٰ سُنَ كُوكَا، حَرْ أَنَ عِيَ جِنْ مُرْيَرْسُ ثَنْ أَ يَهَظَ؞ حَرْ مَا سُواْجُواْجِنْ مُواْوَبْ سُنَ إِيهُ سَبُواْدَ سُنْ ڢِدَّ ذُوثِيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen Heshbon da na Eleyale suka yi kuka da ƙarfi, har ana iya jin kukansu daga Yahaza. Har mayaƙa ma sun yi rawar jiki, zuciyarsu ta karai.