Isaiah 16:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَنْذُ إِنَ كُكَ عَكَنْ غُواْنَكِنْ إِنَبِنْ سِبْمَ، كَمَرْ يَدَّ نَيِ عَكَنْ نَ يَظٜىٰرْ؞ يَا هٜىٰشْبُوانْ دَ عٜىٰلٜىٰيَلٜىٰ، ذَنْ ظُبْدَ هَوَيٜىٰنَ عَكَنْكُ، غَمَا إِيهُنْكُ أَ لُواْكَثِنْ غِرْبِنْ یَیَنْ إِتَاثٜىٰنْكُ دَ نَلُواْكَثِنْ غِرْبِنْ حَڟِنْكُ سُنْ ٻَثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu ina kuka saboda gonakin inabin Sibma kamar yadda na yi wa na Yazar. Na zub da hawayena saboda Heshbon da Eleyale, domin ba a sami kaka mai albarka ba, wadda za ta sa mutane yin murna.