Isaiah 17:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kun manta da Allah Mai Cetonku; ba ku tuna da Dutse, kagararku ba. Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا يَا إِسْرَٰٓءِيلَ، كِنْ مَنْتَادَ اللَّهْ ، اللَّهْ مَيْ ثٜىٰتُوانْكِ، بَاكِ تُنَ دَ دُوڟٜىٰ، دُوڟٜىٰنْ ٻُيَنْكِبَ؞ شِيَسَا كُواْ كِنْ دَسَ عِتَتُوَ مَڢِے ݣَوْ دُوانْ سُجَّدَ غَ وَنِ اللَّهْ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Isra'ila, kin manta da Allah wanda ya kuɓutar da ke, wanda ya kāre ki kamar babban dutse. Kin dasa wa kanki lambuna masu ni'ima don ki yi wa gumaka sujada.