Isaiah 17:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk da haka waɗansu kala za su ragu, sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun, aka bar ’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai ’ya’ya,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَطَنْ نٜىٰ نَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا ذَاعَ بَرِ كَمَرْ ضَغُواْوَرْ یَیَ بِيُ كُواْ عُكُ نَیَیَنْ إِتَاثٜىٰنْ ظَيْتُنْ دَ عَكَ كَكَّٻٜىٰ، كَمَرْ ضَغُواْوَرْ حُطُ كُواْ بِيَرْ أَ رَسَّ مَڢِے نٜىٰسَ نَ إِتَاثٜىٰ مَيْ بَادَ یَیَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ نَا ڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Isra'ila kuma za ta zama kamar itacen zaitun wanda aka karkaɗe 'ya'yansa, aka bar biyu ko uku kawai a ƙwanƙolin itacen, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassansa. Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na faɗa.”