Isaiah 18:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama kafin girbi, sa’ad da furanni suka karkaɗe furanni kuma suka zama ’ya’yan inabin da suka nuna, zai faffalle rassan kuringar inabi da wuƙa, ya yanke ya kuma kwashe rassan da suka bazu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَاڢِنْ لُواْكَثِنْ غِرْبِنْ یَیَنْ إِنَبِے، لُواْكَثِنْ دَ ڢُلَوَ دُكَ سُكَ كَكَّٻٜىٰ، يَايِنْ دَ یَیَنْ إِنَبِے سُكَ ڢَارَ نُونَ، أَ لُواْكَثِنْ ذَاعَ هَلَّكَ إِتِيُواْڢِيَ، كَمَرْ يَدَّ عَكٜىٰ يَيَّنْكَ رَسَّنْ إِتَاثٜىٰنْ إِنَبِے دَ وُڧَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kafin a tattara 'ya'yan inabi, sa'ad da furanni duka suka karkaɗe, 'ya'yan inabi suna ta nuna, haka magabta za su hallaka Habasha a sawwaƙe kamar yadda ake faffalle rassan kurangar inabi da wuƙa.