Isaiah 18:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan lokaci za a kawo kyautai wa Ubangiji Maɗaukaki daga dogayen mutane masu sulɓin jiki, daga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko na jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba. Za a kawo kyautai zuwa Dutsen Sihiyona, wurin da Sunan Ubangiji Maɗaukaki yake.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ لُواْكَثِنَّنْ ذَاعَ كَٰوُاْ وَ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ݣَوْتَيْ دَغَ دُواْغَيٜىٰنْ مُتَنٜىٰ مَاسُ لَوْشِنْ جِكِے، وَطَنْدَ عَكٜىٰ جِنْ ڟُواْرُوانْسُ كُواْعِنَ عَدُونِيَا، دَغَ أَلْعُمَّ مَيْ ڧَرْڢِے دَ إِيكُواْ، دَغَ ڧَسَرْ نَنْ دَ كُواْغُنَ سُنْ رَبَ؞ ذَاسُ كَٰوُاْ ݣَوْتَيْ عَتُدُنْ سِهِيُواْنَ، وُرِنْ ذَمَنْ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan lokaci Ubangiji Mai Runduna zai karɓi hadayu daga wannan ƙasa, a mafarin Kogin Nilu, wato wannan ƙaƙƙarfar al'umma mai iko, waɗannan dogayen mutane masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya. Za su zo Dutsen Sihiyona, inda ake yi wa Ubangiji Mai Runduna sujada.