Isaiah 19:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Zan tā da hargitsi tsakanin mutumin Masar da mutumin Masar, ɗan’uwa zai yi gāba da ɗan’uwa maƙwabci ya yi gāba da maƙwabci, birni ya yi gāba da birni, mulki ya yi gāba da mulki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، «ذَنْ ذُغَ مُتُمِنْ مَصَرْ عَكَنْ وَنِ مُتُمِنْ مَصَرْ، طَنْعُوَ ذَيْ يِڢَطَ دَ طَنْعُوَنْسَ، مَڨُوبْثِ كُمَ دَ مَڨُوبْثِنْسَ، بِرْنِ ذَيْ يِڢَطَ دَ بِرْنِ، مُلْكِ كُمَ ذَيْ يِڢَطَ دَ مُلْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce, “Zan ta da hargitsi a yi yaƙin basasa a Masar, ɗan'uwa ya yi gāba da ɗan'uwa, maƙwabci kuma gaba da maƙwabci. Biranen da suke hamayya za su yi faɗa da juna, sarakunan da suke hamayya kuma za su yi faɗa saboda neman iko.