Isaiah 22:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasa mai girma. A can za ka mutu a can kuma kekunan yaƙinka masu daraja za su kasance, abin kunya kake ga gidan maigidanka!
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ نَطٜىٰكَ يَجٜىٰڢَرْ دَكَيْ عَثِكِنْ ڧَسَا مَيْ ڢَاطِ؞ عَثَنْ ذَاكَ مُتُ كُسَدَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ دَ كَكٜىٰ تَاڧَمَ دَسُو؞ أَبِنْ كُنْيَا كَكٜىٰ أَغِدَنْ مَيْغِدَنْكَ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka!